Rasha da Ukraine sun amince a tsagaita wuta
Shugabannin kasashen Rasha da Ukraine da Faransa da Jamus sun bayyana takaicinsu game da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka karya tsakanin bangarorin da ke rikici a Ukraine bayan shugabannin hudu sun zanta ta wayar tarho a tsakaninsu.
Wallafawa ranar:
Shugabannin kasashen sun yi kira a mutunta yarjejeniyar da suka amince a birnin Minsk na Belarus a ranar 12 ga watan Fabrairu, hadi da janye manyan makamai da sakin fursononi.
Kafin zantawar, Shugaban Kasar Ukraine Petro Poreshenko ya bukaci Majalisar Dinkin Duniya ta girke dakarunta a gabashin kasar da ‘Yan tawaye ke iko don tababtar da aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar da suka kulla da yan tawayen kasar.
Shugaban ya ce sojojin z asu taimaka wajen ganin ba a samu matsalar da ake fuskanta ba ta karya yarjejeniyar.
Majalisar tsaron kasar ta amince da bukatar shugaban.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu