Kwamandan askarawan Ukraine ya tabbatar da nasarar da Rasha ke samu a kansu
Babban kwamandan Sojin Ukraine ya ce Dakarun Rasha na ci gaba da yin galaba akan su.Janar Oleksandr Syrskyi, ya bayyana haka ne da yammacin ranar Lahadi a wani sako da ya wallafa a shafin sa na Facebook.
Wallafawa ranar:
Kalaman na sa na zuwa ne yayin da Dakarun Rasha ke ci gaba da kai musu hare-hare musamman a yankin gabashin Donetsk.
A cewarsa sojojin Ukraine sun ja da baya, tare da amincewa da mika wasu yankuna ga ƴan Rasha.
Wani gari da Rasha ta kwace
Dama dai a ranar Lahadi ma'aikatar tsaron Rasha ta ce dakarunta sun kwace kauyen Novobakhmutivka da ke gabashin yankin Donetsk mai tazarar kilomita 10 daga arewacin Avdiivka, wanda ta kwace tun a watan Fabrairu.
Yanzu haka dai kasar Ukeraine na fafutukar daukar isassun sojoji da za su maye gurbin wadanda suka kwanta dama ko suka ji muggan raunuka a yakin da aka shafe tsawon lokaci a gwabzawa kusan shekaru uku.
Kazalika Ukraine din na jiran isar makaman biliyoyin daloli daga Amurka wanda take fatan kawo karshen karancinsu na tsawon watanni domin ta zamo gagarabadau a fagen daga.
Tun a farkon watan nan shugaban hukumar leken asirin Ukraine Kyrylo Budanov ya yi hasashen cewa dakarun na Ukraine za su fuskanci yanayi mafi wahala a tsakiyar watan Mayu zuwa farkon watan Yuni.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu