Isa ga babban shafi

Turkiyya ta dakatar da kasuwanci da Isra'ila har sai ta tsagaita wuta a Gaza

Turkiyya ta ce ta dakatar da duk wata huldar kasuwanci tsakaninta da Isra'ila har sai an tsagaita bude wuta a yakin da ake yi a Gaza.

Recep Rayyip Erdogan shugaban Turkiyya.
Recep Rayyip Erdogan shugaban Turkiyya. AFP - GENT SHKULLAKU
Talla

Ana hasashen adadin cinikayya tsakanin kasashen biyu ya kai dala bilyan bakwai a shekarar bara.

Ma'aikatar kula da harkokin kasuwanci ta Turkiyya ta ce za’a aiwatar da matakin har sai Isra'ila ta bayar da damar shigar da kayan jin kai zuwa Gaza ba tare da matsala ba.

Ministan harkokin kasuwanci na Turkiyya, Omer Bolat ya ce duba da yadda Isra’ila ta ƙi ɗaga ƙafa, kuma take barazanar kutsa kai cikin birnin Rafah na kudancin Gaza, saboda haka, Turkiyya ta dakatar da duk wata huldar shigowa ko fitar da kayayyaki dac Isra’ila.

Sai dai bayan fitar wannan sanarwar ministan harkokin wajen Isra'ila ya zargi shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan da kasancewa mai mulkin kama karya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.