Isa ga babban shafi

Adadin wadanda suka mutu a ambaliyar ruwa da zaftarewar ƙasa a Brazil ya kai 58

Adadin mutane da suka mutu a kudancin Brazil sakamakon ambaliyar ruwa da zaftarewar ƙasa da suka auku sakamakon mamakon ruwan sama ya kai 58, kana wasu 67 da suka ɓata, kamar yadda hukumar tsaron farin kayan ƙasar ta bayyana.

Wasu motoci kenan da ambaliyar ta cim musu a birnin Rio Grande do Sul. (03/05/2024).
Wasu motoci kenan da ambaliyar ta cim musu a birnin Rio Grande do Sul. (03/05/2024). REUTERS - Diego Vara
Talla

Tumbatsar madatsun ruwa a jihar Rio Grande do Sul na barazana ga cikin birnin Porto Alegre, inda mahukunta ke ƙoƙarin kwashe wasu mutane da muhallansu ke cikin ruwa tsamo-tsamo.

Masu aikin ceto dai na fuskantar aiki mai sarkakiya, sakamakon yadda ruwa ambaliya ta mamaye tare da datse hanyar shiga garin.

Kogin Guaiba, wanda ya ratsa birnin Porto Alegre ya cika ya batse irin yadda ba a taba gani ba a tarihi, inda ya kai kafa 16, wanda rabon da a samu haka tun a shekarar 1941.

Mahukunta na koƙarin kwashe al’ummomin da yankunansu ke kusa da ruwa, inda a cikin wata sanarwa su ka ce duk da yadda yanayi ya yi matuƙar muni, ana nan ana ci gaba da aiki ceto.

shugaba Luiz Inacio Lula da Silva a shafinsa na X ya wallafa wani hoton bidiyon jirgi mai sauka yana sauke wani jami’in soji a kan rufin wani gida, a ƙoƙarinsa na ceto wata jaririya da aka lulluɓe a cikin wani bargo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.