Isa ga babban shafi

Zanga-zangar daliban da ke tir da harin Isra'ila a Gaza na bazuwa a sassan Turai

Yayin da Isra’ila ke ci gaba da kai farmaki a sassan Zirin Gaza, daruruwan dalibai ne a kasashen Turai ke ci gaba da zanga-zangar nuna goyon bayansu ga Falasdinawa da kuma Allah wadai da irin hare-haren da kasar ke kaddamarwa, wato tun daga ranar 17 ga Afrilu akalla jami’o’in Amurka guda 40 ne dalibai suka kafa tantuna, a zanga-zangar adawa da abin da Isra’ilan ke aikatawa a Gaza.

Yadda dalibai suka gudanar da zanga-zanga a jami'ar George da ke birnin Washington a kasar Amurka, ranar 25 ga Afrilu, 2024.
Yadda dalibai suka gudanar da zanga-zanga a jami'ar George da ke birnin Washington a kasar Amurka, ranar 25 ga Afrilu, 2024. © Alex Wong/Getty Images via AFP
Talla

Kusan mutum 2,000 aka tsare a kasar ta Amurka, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka bayyana.

A kasar Faransa kuwa, ‘yan sanda ne suka yi amfani da karfin tuwo wajen fatattakar masu zanga-zangar adawa da abinda Isra’ila ke aikatawa a Gaza, tare da cafke akalla mutum 91 a jami’ar kimiyya ta Po da ke birnin Paris.

A Jami’ar Humboldt da ke tsakiyar birnin Berlin na kasar Jamus, jami’an tsaro sun tilastawa masu zanga-zanga sauya wuri, bayan sun kafa tantuna, inda hukumomin kasar ke fargabar abin da ya faru a kasashen Amurka da Birtaniya ko kuma Faransa suma ya shafe su.

A Canada, bayanai sun ce dalibai sun gudanar  da makamanciyar wannan zanga-zanga a biranen Montreal, Ottawa, Toronto, da Vancouver, kuma sun sha alwashin ci gaba da gudanarwa har sai hukumomin kasar sun yanke alaka da Isra’ila.

Haka wannan al’amari ya kasance a kasashen Asutralia da Ireland, inda daruruwan dalibai suka yi fitar dango, suna me rera wakokin goyon bayan ga al’ummar Falasdinu

Yayin da gomma dalibai suka fito zanga-zangar neman gwamnatin kasar Mexico ta yanke duk wata alaka da Isra’ila tare da bayyana goyon baya ga Falasdinawa, daruruwan dalibai ne suka tare kofar shiga jami’ar Lausanne da ke Switzerland tun ranar Juma’a, bisa neman a tsagaita wuta a Gaza cikin gaggawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.