Isa ga babban shafi

Zanga-zangar goyan bayan Faladinawa na samun ƙarbuwa a jami'o'in Amurka

Ƴan sandan Amurka sun tsare mutane kusan 200 a wasu  jami'o'in ƙasar uku ranar Asabar, a wani yankuri na dakile zanga-zanar goyan bayan Falasdiwa da ke yawaita a jami’o’in Amurka.

Zanga-zangar goyon bayan Falasdinu a jami'o'in Amurka ya bazu a fadin kasar - Afrilu 26, 2024
Zanga-zangar goyon bayan Falasdinu a jami'o'in Amurka ya bazu a fadin kasar - Afrilu 26, 2024 © REUTERS
Talla

Ƴan sanda a Boston sun tsare mutane kusan 100 a lokacin da suke share wani sansanin zaman dirshen a jami'ar Arewa maso Gabas, inda hotuna a shafukan sada zumunta suka nuna jami'an tsaro na loda tantuna a bayan wata babbar mota.

An dauki matakin ne bayan da wasu masu zanga-zangar suka yi amfani da kalaman batanci irin na kyamar Yahudawa, ciki har da kira a kawar da Yahudawa.

 'Ƴan sandan jami'ar jihar Arizona ma sun kama mutane 69 bayan da suka kafa wasu tantuna a harabar jami'ar.

A  jami'ar Indiana kuwa an kama mutane 23 yayin da suke share sansanin zanga-zangar a harabar jami'ar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.