Isa ga babban shafi

Arsenal ta sake lallasa Bournemouth da ci 3 - 0 a gasar firimiya

Duniya – Kungiyar kwallon kafar Arsenal na ci gaba da jan zarenta yadda take so a gasar firimiya ta Ingila ganin yadda ta lallasa kungiyar Bournemouth da ci 3-0 a karawar da suka yi yau asabar.

Bukayo Saka da Declan Rice suna murnar nasarar da suka samu
Bukayo Saka da Declan Rice suna murnar nasarar da suka samu © AP - Kin Cheung
Talla

Wannan nasarar ta sanya Arsenal ta bai wa abokiyar adawar ta Manchester City tazarar maki 4 a teburin firimiya, kafin karawar da City za tayi yammacin yau da kungiyar Wolverhampton da kuma kwantan wasanta guda daya.

Bukayo Saka ya fara jefawa Arsenal kwallon ta na farko sakamakon bugun fenariti a mintina 45, yayin da Leandro Trossard da Declan Rice suka jefa sauran kwallaye 2 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci domin tashi wasan da ci 3-0.

Leandro Trossard
Leandro Trossard © AP - Zac Goodwin

Alkalin wasan ya soke kwallon da Gabriel ya jefa saboda abinda yace satar fage, amma matakin bai hana kungiyar Arsenal kwashe maki 3 da aka warewa wannan karawar ba.

Yanzu haka Arsenal na da maki 83 daga wasanni 36 da ta buga a matsayi na farko, yayin da Manchester City dake matsayi na 2 ke da maki 79, sai kuma Liverpool a matsayi na 3 da maki 75.

Wasanni guda 2 da suka ragewa Arsenal a wannan kakar sun hada da karawar da za suyi da Manchester United a makon gobe, sai kuma karawa da Everton a ranar kammala gasar Firimiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.