Isa ga babban shafi
Amurka-Rasha

Amurka ta gargadi Rasha akan Ukraine

Kasar Amurka ta zargi Rasha da ‘Yan tawayen Ukraine da laifin rusa yarjejeniyar tsagaita wuta da aka amince domin kawo karshen zubar da jini a gabacin Ukraine, bayan sabon fada ya barke a garin Debaltseve.

Dakarun Ukraine a yankin Debaltseve.
Dakarun Ukraine a yankin Debaltseve. REUTERS/Gleb Garanich
Talla

Rahotanni sun ce ‘Yan tawaye sun kori dakarun gwamnatin Ukraine daga garin Debaltseve.

Amurka ta ce zata dauki mataki akan Rasha bayan shugaba Putin ya yi kira ga dakarun Ukraine a gabacin kasar su mika kansu.

Tuni Ukraine ta yi kira ga kasashen yammaci su dauki mataki akan Rasha bayan ‘Yan tawayen da ke goyon bayanta sun abkawa daruruwan dakarun kasar a lokacin da yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki uku ta fara aiki.

A birnin Minsk na Belarus ne kasashen Faransa da Jamus suka jagoranci zaman sulhu tsakanin Ukraine da Rasha inda suka amince da yarjejeniyar tsagaita wuta domin kawo karshen rikicin kasar da shafe tsawon watanni 10 ana zubar da jini.

Rahotanni daga gabacin Ukraine na cewa yanzu haka shugaban ‘Yan tawayen kasar yana kwance a gadon asibiti yana jinya sakamakon raunin da ya ji a wata musayar wuta da dakarun gwamnati a Donetsk.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.