Isa ga babban shafi
Ukraine-Rasha

Yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Ukraine da 'yan tawaye

Gwamnatin Ukraine da kuma ‘yan tawayen da ke goyon bayan Rasha, sun kulla yarjejeniyar tsagaita wuta a taron sulhun da kasashen duniya suka shirya a birnin Minsk na kasar Belrus.

Taron Minsk kan Ukraine
Taron Minsk kan Ukraine AFP
Talla

A karkashin wannan yarjejeniya dai bangarorin biyu sun amince da soma yin aiki da shirin tsagaita wutar daga ranar 15 ga wannan wata na Fabarairu, yayin da kowanne daga cikinsu zai janye manyan makamansa daga yankunan da ake takaddama a kai.

An dai cimman wannan sulhu ne a taron da aka gudanar lokacin tattaunawar zaman lafiya da shugaban Faransa Francois Hollande da Waziriyar kasar Jamus Angela Merkel, da shugaba Vladimir Putin na Rasha da kuma Petro Poroshenko na Ukraine suka halarta.

Bayan tsagaita wuta kuwa sai batun yin musayar fursunoni tsakanin bangarorin biyu wanda za a soma a ranar 19 ga wannan wata na Fabarairu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.