Isa ga babban shafi

Pedro Sanchez na tunanin yin murabus bayan kaddamar da bincike a kan matarsa

Firaministan Spain Pedro Sanchez a yau Laraba a wata wasika da aka buga ya na mai sanar da aniyarsa na sauka daga mukaminsa mudin aka gano cewa matarsa na da hannu a zargin cin hanci da rashawa.

Firaministan Spain Pedro Sanchez da mai matarsa Begona Gomez
Firaministan Spain Pedro Sanchez da mai matarsa Begona Gomez © Yves Herman / Reuters
Talla

Rahotanni daga kasar ta Spain na dada nuni ta yada jama’a suka shiga wani yanayi na rudani bayan sanarwar Firaministan kasar ta Spain,sanarwar da ke zuwa yan lokuta bayan da alkalin alkalan kasar ya bayar da umurni kaddamar da wani bincike na farko kan zargin cin hanci da rashawa da ake yi wa matar Pedro Sanchez, Begona Gomez.

Firaministan kasar ya bukaci daukar gajeren lokaci don yi tunani dangane da makomarsa a siyasance.

Firaministan Spain Pedro Sanchez da matarsa Begona Gomez
Firaministan Spain Pedro Sanchez da matarsa Begona Gomez © Yves Herman / Reuters

Sanchez na mai bayyana cewa "ko zan ci gaba da kasancewa a kan gwamnati ko sauka daga wannan mukami nan gaba.

Firaministan Spain ya bayyana ranar Litinin 29 ga Afrilu a matsayin ranar da zai gabatarwa yan kasar da matsayinsa na ci gaba da kasancewa a kan wannan kujera ko kuma sauka daga mukamin Firaminista.

An kaddamar da wannan binciken ne ranar 16 ga watan Afrilu bayan wani korafi daga kungiyar "Manos limpias", kungiyar da aka yi la'akari da ita da kuma kusanci da ‘yan adawa, ta sanar a cikin wata gajeriyar sanarwa a Madrid.

Firaministan Spain Pedro Sanchez
Firaministan Spain Pedro Sanchez AP - Jean-Francois Badias

A cikin wasika daga Firaministan kasar, Pedro Sanchez, wanda ke kan mulki tun daga 2018, ya yi tir da korafin da kuma hanyoyin da was uke amfani da shi don shafa masa kashin kaji da kuma amfani da iyalansa.

 Firaministan Spain ya bayyana cewa y ana sane da cewa suna shigar da kara a kan matarsa Begona, ba wai don ta aikata wani abu da ya saba wa doka ba, domin sun san cewa wannan ba gaskiya ba ne, amma don ita ce matarsa.

Pedro Sanchez ,Firaministan Spain
Pedro Sanchez ,Firaministan Spain AP - Bernat Armangue

A cewar kafar yada labaran El Confidencial ta yanar gizo, wadda ta bankado labarin, wannan bincike ya mayar da hankali ne musamman kan alakar Begona Gomez da kungiyar masu yawon bude ido ta kasar Spain Globalia, mai kamfanin jiragen sama na Air Europa, a daidai lokacin da shugaban ke tattaunawa da gwamnati.

'Yan adawa na hannun dama a yau Laraba sun yi kira ga Firayiminista da ya "ba da bayani ga mutanen kasar’’,matakin da makusantar Firaministan Spain suka tabbatar da bayar da bahasi nan gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.