Isa ga babban shafi

EU ta koka da jan kafar da ake wajen tallafawa Ukraine a yakinta da Rasha

Ministocin ƙasashen Ƙungiyar Tarayyar Turai EU, sun ce ya zama dole su gaggauta cika alƙawuran da suka ɗauka na bai wa Ukraine tallafin makamai, domin ɗorawa kan gagarumin taimakon da Majalisun Dokokin Amurka suka amince a miƙa wa ƙasar ta Ukraine.

Wani taron ministocin kasashen EU a Brussels.
Wani taron ministocin kasashen EU a Brussels. AFP - JOHN THYS
Talla

Daga cikin ministocin ƙasashen ƙungiyar ta EU da suka koka kan jan ƙafar da ake fuskanta dangane da cika alkawuran taimaka wa Ukraine, akwai ministar harkokin wajen Latvia Baiba Braze, wadda ta ce bai kamata a cigaba da ɓata lokaci wajen gudanar da taruka ba tare da aiwatar da muhimman matakan da suke cimma matsaya kansu ba.

Taron ministocin manbobin na EU a Luxemborg na zuwa ne bayan da a ranar Asabar ‘yan Majalisun Dokokin Amurka suka amince da ware dala bliyan 61 da za a tallafa wa Ukraine da su a yakin da take fafata wa da Rasha, shirin da sai da aka shafe watanni shida ana taƙaddama kansa tsakanin gwamnati da ‘yan majalisun kafin amincewa da shi.

Ɗaya daga cikin muhimman buƙatun da Ukraine ta daɗe tana miƙa wa ƙasashen Turai shi ne neman taimakon nau’rorin tsaron sararin samaniya, don kare kanta daga hare-haren makamai masu lizamin da Rasha ke auno mata, burin da har yanzu bai cika ba.

Ya zuwa yanzu Jamus ce ƙasa ɗaya tilo daga cikin ƙungiyar EU da a baya bayan nan, ta amsa kiran Ukraine na aika mata da ƙarin na’urorin tsaron sararin samaniyar da take nema.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.