Isa ga babban shafi

Kotun Faransa ta tabbatar da tuhumar da ake yiwa Francois Fillon

Kotun daukaka kara ta tabbatar da tuhumar da ake yiwa Francois Fillon a yau Laraba 24 ga watan Afrilu a shari’ar samar da ayyukan bogi da kuma baiwa matarsa damar gudanar da wasu ayyuka a lokacin da ya ke da mukamin Firaminista ,wanda ya sabawa dokokin kasar ta Faransa.

Francois Fillon tsohon Firaministan Faransa a harabar kotu
Francois Fillon tsohon Firaministan Faransa a harabar kotu AFP/File
Talla

Alkalan kotun a wannan zama sun bukaci kotu ta sake gudanar da wani sabon zama inda ake sa ran yanke masa hukunci da kuma biyan diyya.

An tabbatar da hukuncin da aka yanke wa wasu mutane biyun da ake tuhuma da suka hada da matarsa ​​Pénélope Fillon sai dai sun shigar da kara kan hukuncin da kotun daukaka kara ta birnin Paris ta yanke a kan su.

Tsohon Firaministan Faransa François Fillon
Tsohon Firaministan Faransa François Fillon © Charles Platiau, Reuters

 A ranar 9 ga watan Mayun shekarar 2022 ne aka yanke wa Francois Fillon da ya rike mukamin shugaban gwamnati daga shekara ta 2007 zuwa 2012, a karkashin shugabancin Nicolas Sarkozy, a kan kararrakin daurin shekaru hudu a gidan yari, ciki har da shekara guda, da tarar Yuro 375,000 da kuma daurin shekaru 10 a gidan yari.

Bisa ga hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke, za a iya yanke hukuncin gidan yari a tsarin zama gida karkashin kulawar hukuma.

Penelope Fillon, l'épouse matar tsohon Firaministan Faransa Francois Fillon
Penelope Fillon, l'épouse matar tsohon Firaministan Faransa Francois Fillon JEAN-FRANCOIS MONIER / AFP

An tabbatar da hukuncin Penelope Fillon da Marc Joulaud a wannan zama na yau Laraba,inda kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin da aka yanke wa mai dakin Francois Fillon, Penelope Fillon (dakatar da hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari da kuma tarar Yuro 375,000) da na mataimakin François Fillon a majalisar dokokin kasar, Marc Joulaud, (dakatar da zaman gidan yari na shekaru uku). Wadanda ake tuhumar, wadanda a kodayaushe suna ci gaba da kasancewa ba su da laifi, an kuma umurce su da su biya jimillar kudin da ya kai Euro 800,000 a matsayin diyya ga majalisar dokokin kasar.

François Fillon, tare da mai dakin sa Penelope Fillon
François Fillon, tare da mai dakin sa Penelope Fillon AP - Thibault Camus

A shekara 2017 ne wata jarida a kasar ta Faransa mai suna  Le Canard Enchainé ta falasa labarin samar da ayyukan bogi da almubazzaranci da kudaden jama'a a karkashin kulawar matar  François Fillon wanda a lokacin ya kasance dan takara na dama a zaben shugaban kasar ta Faransa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.