Isa ga babban shafi

Kasashen Amurka da Birtanya da wasu 16 sun bukaci tsagaita buda wuta a Gaza

Amurka da Birtaniya da wasu ƙasashe 16 sun bukaci gaggauta tsagaita wuta a yaƙin Gaza domin samun damar ceto mutanen da Hamas ke garkuwa da su tun bayan da harin ta ƙungiyar ta kai cikin Isra’ila ranar 7 ga watan Oktaban bara, kamar yadda zaku ji cikin rahotan wanda ke kunshe a cikin wata wasika da aka fitar a ranar Alhamis.

Wasu Amurkawa da suka rina hannayensu da launin jini a zauren majalisar dokokin Amurka, domin nuna adawa da hare-haren Isra'ila kan Zirin Gaza.
Wasu Amurkawa da suka rina hannayensu da launin jini a zauren majalisar dokokin Amurka, domin nuna adawa da hare-haren Isra'ila kan Zirin Gaza. REUTERS - KEVIN LAMARQUE
Talla

Fadar White House ta Amurka ce ta fitar da wata wasikar ta hadin gwiwa da shugabannin kasashe 18 suka sanya wa hannu, inda suka bukaci a sako mutanen da kungiyar Hamas ta yi garkuwa da su, tare da bukatar tsagaita wuta na dogon lokaci a rikicin da ya lakume rayukan Falasdiwa a yankin Zirin Gaza da kewaye.

Wasikar tana cewa:

Muna kira da a gaggauta sakin ɗaukacin mutanen da Hamas ke garkuwa da su a Gaza sama da kwanaki 200. Sun ƙunshi ƴan ƙasashenmu. Makomar mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma fararen hula a Gaza, wadanda ke samun kariya a karkashin dokokin ƙasa da ƙasa, na zama abin matuƙar damuwa a duniya.

Sun jaddada cewar, yarjejeniyar da aka cimma kan sakin mutanen da aka yi garkuwa da su, za ta kai ga tsagaita wuta na dogon lokaci a Gaza, wanda zai sauwaka ayyukan taimakon jin kai da za a shigar fadin Gaza, da kuma koƙarin kawo karshen yakin, domin mazauna Gaza su iya komawa gidajensu.

 

Sun kuma nuna goyon bayan su ga shiga tsakanin da ake yi domin domin ganin mutanen sun goma gida. Tare da kira ga Hamas ta kai zuciya nesa domin kawo karshen rikicin wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali mai ɗaurewa a yankin.

Ƙasashen da suka sanya hannu cikin wasiƙar ta hadin guiwa sun hada da Amurka da Argentina da Austria da Brazil da Bulgaria da Canada da Colombia da kuma Denmark.

Sauran ƙasashen da suka bukaci sakin mutanesu da ke hannun ƙungiyar Hamas a Gaza da kuma bukatar tsagaita wuta sun hada da Faransa da Jamus da Hungary da Poland da Portugal da Romania da Serbia da Spain da Thailand da kuma Burtaniya.

A nata bangaren, alamu na nuna cewa Isra'ila na shirin kai farmaki ta ƙasa yankin Rafah da ke kudancin Gaza, inda kafafen yada labaran Isra'ila suka rawaito cewa, Rundunar sojin ƙasar ta shaidawa gwamnati cewa a shirye take da dai jiran umarni ne kawai domin fara farmakin, yayin da majalisar tsara yake-yaken Benjamin Netanyahu na tattauna domin shirya farmakin.

Iyalan ƴan ƙasar Isra'ila da aka yi garkuwa da su ɗin dai na ci gaba da matsawa gwamnatin Netanyahu lamaba domin ganin an tsagaita wuta, watakila ya zama silar sakin ƴan uwansu.

Hamas da sauran kungiyoyin da ke fafutukar ƴancin Falasdinawa sun yi garkuwa da mutane kusan 250 tun  ranar 7 ga watan Oktoba lokacin da suka aki hari har cikin Isra’ila.

An sako 105 daga cikinsu a wani bangare na yarjejeniyar musayar fursunoni da akayi a watan Nuwambar bara. babu dai tabbas kan ko nawa ke raye daga cikin sauran wadanda ke tsare a hannun masu garkuwa da su a yankin Gaza kawo yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.