Isa ga babban shafi

Mutane kusan dubu 37 sun bace a Ukraine sakamakon mamayar Rasha

Gwamnatin Ukraine ta alƙaluman da ta tattara sun nuna cewar mutane kusan dubu 37 ne suka bace, waɗanda kuma har yanzu babu alamun za a sake jin ɗuriyarsu, tun bayan da Rasha ta ƙaddamar da yaƙin neman mamaye kasar a watan Fabarairun shekarar 2022.

Wasu 'yan kasar UKraine a birnin Kyiv, da ke zanga-zanga kan ɓacewar gwamman 'yan uwa da abokan arzƙinsu da suka bace sakamakon yakin da Rasha ta kaddamar kan kasa a watan Fabarairun shekarar 2022. 16 ga Oktoba, 2023.
Wasu 'yan kasar UKraine a birnin Kyiv, da ke zanga-zanga kan ɓacewar gwamman 'yan uwa da abokan arzƙinsu da suka bace sakamakon yakin da Rasha ta kaddamar kan kasa a watan Fabarairun shekarar 2022. 16 ga Oktoba, 2023. © Sergei Supinsky, AFP
Talla

Mahukuntan na Ukraine sun yi gargaɗin cewa mai yiwuwa adadin mutanen da suka yi ɓatan dabon cikinsu harda sojojin kasar, ka iya zarce adadin da suka bayyana da tazara mai yawa.

Yanzu haka dai kimanin kashi 1 bisa 5 na faɗin kasar Ukraine ne ke karkashin ikon sojojin Rasha, bayan shafe sama da shekaru biyu suna fafata yaƙi da dakarun kasar.

Ƙungiyoyin kare haƙƙin dan Adam da dama ne suke zargin sojojin Rasha da ɓatar da mutane da dama, gami da sace ƙananan yara da dama a yankunan Ukraine da suka ƙwace, sai dai gwamnatin Rashan na cigaba da yin watsi da zarge-zargen.

Wani rahoto da hukumar kare haƙƙin dan Adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta fitar a watan Maris, ya ce  aƙalla mutane dubu 10 da 810 aka kashe, tun bayan yaƙin da Rasha ta kaddamar kan Ukraine, cikinsu har da mutanen dubu 8 a yankunan da basu kuɓucewa dakarun kasar ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.