Isa ga babban shafi

Leonel Messi ya dawo taka leda bayan dawowarsa daga jinya

Bayan dawowar Lionel Messi daga jinya, ya yi nasarar jefawa kungiyarsa ta Inter Miami kwallo a ragar Colorado Rapids a wani wasa da suka kara.

Gwarzon dan wasan Argentina a kungiyarsa ta Inter Miami da ke wasa a Amurka.
Gwarzon dan wasan Argentina a kungiyarsa ta Inter Miami da ke wasa a Amurka. AP - Erik Verduzco
Talla

Zura kwallon da Messi ya yi sanya kungiyar ta yi canjaras da abokiyar karawarta ta Colorado Rapids yayin da suka tashi da ci 2-2.

Dan wasan dan kasar Argentina dai bai samu damar buga wasanni hudu ba a sakamakon raunin da ya samu, kuma bayan dawowa daga hutun rabin lokaci sai kungiyar tasa ta jefa 1-0 bayan bugun daga kai sai mai tsaron gida da  Rafael Navarro ya jefa.

Mesin ne dai ya taimaka wajen kara zura kwallo a ragar Colorado Rapids a yayin da ya ba wa Leonardo Afonso da suke kungiya daya.

Kungiyar Miami dai ba ta kai ga samun nasara ba a wasan yayin da dan wasan kungiyar Colorado Rapids ya antayawa Inter Miami kwallo a raga wadda ta sanya aka tashi  canjaras wato ci 2-2.

Miami ta gagara ci gaba da jan ragamar wasan ne dai bayan da Cole Bassett ya ramawa Rapids a minti na 88 da fara wasan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.