Isa ga babban shafi
Ukraine

Rasha ta amince a shata sabon tsarin sasanta rikicin Ukraine

Shugabannnin kasashen Rasha da Jamus da Faransa sun amince su samar da wani sabon tsari da zai taimaka a kawo karshen rikicin kasar Ukraine. Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel da takwaranta na Faransa Francios Hollande tare Vladimir Putin na Rasha sun amince da matakin ne bayan sun shafe sa’oi suna ganawa ta musamman a birnin Moscow.

Merkel ta Jamus da Putin na Rasha da Hollande na Faransa suna ganawa akan Ukraine
Merkel ta Jamus da Putin na Rasha da Hollande na Faransa suna ganawa akan Ukraine REUTERS/Maxim Zmeyev
Talla

Kasashen sun amince su shata matakan kawo karshen rikicin tare da kudirorin da shugaban Ukraine Petro Poroshenko zai gabatar.

Amma babu wani cikakken bayani game da kudirorin da kuma matakan da kasashen zasu dauka domin kawo karshen rikicin na Ukraine da ya lakume rayukan mutane sama da 5,000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.