Isa ga babban shafi
Ukraine-Amurka-Rasha

Amurka na tunanin baiwa dakarun Ukraine makaman da zasu yaki 'yan tawayen kasar

Yayin da rikincin kasar Ukraine ke ci gaba da zafafa, gwamnatin Amurka na duba dukkan matakan daya dace a bi. Sai dai duk da haka hukumomin na Washington basu cimma matsaya ba, kan yuwuwar aike wa da makamai ga hukumomin birnin Kiev, don yakar ‘yan tawaye masu goyon bayan kasar Rasha.Yayin da ake sa rai da Sakataren Harkokin wajen Amurkan John Kerry zai isa kasar ta Ukraine cikin wannan makon, wasu bayanai na cewa hukumomin birnin Washington da ma Kungiyar tsaro na NATO ko OTAN, suna tunanin aike wa sojan na Ukraine makaman kare kai.Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka Jen Psaki, ta shaida wa manema labaru cewa hukumomin na Washington suna matukar damuwa kan yadda rikicin na Ukraine ke ci gaba da watsuwa, sai dai tace har yanzu basu cimma matsaya ba kan lamarin.Psaki tace Amurkan na duba matakan da take dauka a Ukraine, don tabbatar da cewa sun dace, kuma zasu cimma bukatun kasar.Sai dai Psaki tace wannan ba yana nufin Amurka na neman shiga yakin da ba ruwanta bane da Rasha, illa kawai kasar na naman canza wa Rasha tunaninta ne. 

Wasu dakarun musamman na kasar Ukraine
Wasu dakarun musamman na kasar Ukraine REUTERS/Stanislav Belousov
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.