Isa ga babban shafi
Ukraine

‘Yan tawayen Ukraine sun bayar da sharadi

‘Yan tawayen Ukraine da ke iko da gabacin kasar sun bayar da sharadin cewa ba za su yanye makamansu ba har sai an samu cikakkiyar tsagaita wuta daga bangaren gwamnati, kamar yadda aka tsara a yarjejeniyar tsagaita wuta da suka amince a kasar Belerus.

Dakarun Ukraine suna jiran tsammani bayan yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki
Dakarun Ukraine suna jiran tsammani bayan yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki REUTERS/Gleb Garanich
Talla

‘Yan tawayen sun ce sai idan yarjejeniyar tsagaita wuta ta fara aiki gadan gadan kafin su janye makamansu a fagen yaki, kamar yadda Kamfanin dillacin labaran ‘Yan tawayen a yankin Donetsk na Ukraine ya ruwaito.

Wasu rahotanni daga kasar Ukraine na cewa an samu kwarya-kwaryan tsagaita wuta a aman wutar da ake tsakanin sojojin gwamnati da kuma yan tawayen da ke samun goyan bayan Rasha, kwana biyu bayan fara aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiyar da shugabanin kasashen Faransa da Jamus, Rasha da Ukraine suka kulla.

Amma gwamnatin Ukraine ta ce ba za ta janye makamanta ba saboda babu tabbas daga ‘Yan tawayen kasar.

Karkashin yarjejeniyar da bangarorin biyu suka amince, da misalin karfe 10 na dare ne za su janye makamansu a yau Litinin.

Bisa dukkan alamu dai tsagaita wutar na aiki duk da ‘yan matsalolin da ake fuskanta, a kokarin da ake na ganin an kawo karshen tashin hankalin da aka kwashe watanni 10 ana yi a Ukraine.

Hukumomin kasar sun ce an kashe mutane biyu lokacin da makamin roka ya fada kan garin Popasna a Yankin Lugansk jim kadan bayan fara aiki da yarjejeniyar.

Kakakin gwamnatin kasar Andriy Lysenko ya bayayan fatar ganin an samu kwanciyar hankali bisa abin da suka gani yanzu haka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.