Isa ga babban shafi
Najeriya

NFF: An tsige Maigari

Kwamitin zartarwa na hukumar Kwallon kafa NFF a Najeriya ya tsige Shugaban hukumar Alhaji Aminu Maigari bayan zarginsa da yin almubazzaranci da kudade. Mataimakinsa ne Mike Umeh yanzu aka nada a matsayin shugaban rikon kwarya.

Shugaban hukumar kwallon Najeriya Aminu Maigari
Shugaban hukumar kwallon Najeriya Aminu Maigari Kickoff.com
Talla

Mambobin Kwamitin sun kada wa Aminu Maigari kuri’ar yankan kauna ne bayan sun ce an shafe watanni Takwas ba tare da ya gana da su ba.

Hukumar kwallon Najeriya kuma tace zata sabunta kwangilar Stephen Keshi mai horar da ‘Yan wasan Super Eagles.

Kwamitin Zartarwar hukumar yace sun gamsu da aikin Keshi don haka suka bayar da shawarar a sabunta kwangilar shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.