Isa ga babban shafi

Najeriya: Ya zama wajibi a rika yiwa Malaman jami'o'i gwajin magunguna

Mataimakin shugaban jami’ar Abubakar Tafawa Balewa ATBU dake Bauchin Najeriya mai barin gado Professor Muhammad  AbdulAziz, ya bayyana cewa ya kamata a rika yiwa Malaman jami’o’I gwajin magunguna ba dalibai kawai ba.

Kwayar cutar Bacteria na bijire wa magani a yanzu sabanin a shekarun baya saboda yadda kwayar cutar ke samar da dabarun kare kanta daga tasirin maganin
Kwayar cutar Bacteria na bijire wa magani a yanzu sabanin a shekarun baya saboda yadda kwayar cutar ke samar da dabarun kare kanta daga tasirin maganin Flickr/sparktography
Talla

Shugaban ya yi wannan kira ne a yayin da yake jawabi ga majalisar jami’ar a ranar juma’a da ta gabata.

Malam Abdul’aziz ya kara da cewa bai kamata a rika tilastawa dalibai gudanar da gwajin kwayoyi ba tare da su a suna yi ba, ba tare da suma suna yi ba, domin su kan su basu a wane matsayi suke ba.

A cewar shugaban hakan zai kara tsaftace tsarin jami’o’in da kuma inganta lamura wanda zai bunkasa harkokin ilimi.

Malamin Ya kuma kara da cewa, “Mun tattauna da ma’aikatar ilimi ta tarayya, kuma suna shirin gabatar wa dukkanin jami’o’in kasar cewa kafin kowane dalibi ya kammala rajistar karatu a jami’o’in, ya zama wajibi a yi masa gwajin magunguna.” Domin sanin matsayinsa.

VC din ya yi nuni da cewa, mafi kankantar nasarorin da aka samu a fannonin ci gaban ababen more rayuwa, ci gaban ilimi da kuma hidimar al’umma a lokacin mulkinsa ba zai yiwu ba sai da goyon bayan masu ruwa da tsaki a tsarin, don haka ya ci gaba da cewa wannan tsarin ma sai an hada karfi da karfe kafin a cimma nasara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.