Isa ga babban shafi
MATSALAR TSARO

Wasu 'yan arewacin Najeriya sun yi gargadi a kan girke sojojin Amurka da Faransa

Najeriya – Wasu fitattun 'yan arewacin Najeriya sun bayyana matukar damuwa dangane da yunkurin kasashen Amurka da Faransa na girke sojojin su a cikin kasar, inda suka bukaci gwamnatin kasar da tayi taka tsantsan a kan lamarin.

Austin Lloyd, Sakataren tsaron Amurka
Austin Lloyd, Sakataren tsaron Amurka © Maya Alleruzzo / AP
Talla

A wata budaddiyar wasikar da wadannan fitattun mutane suka rubutawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da shugabannin majalisun tarayyar kasar, sun bukaci shugabannin da su kaucewa amincewa da irin wannan bukata na kwashe sojojin wadannan kasashe daga Sahel zuwa Najeriya.

Daga cikin wadanda suka rattaba hannu a kan wannan wasikar akwai Farfesa Abubakar Siddique Muhammed na Cibiyar Bunkasa Dimokiradiya dake Zaria da Farfesa Kabir Suleiman Chafe, tsohon ministan mai da Farfesa Attahiru Jega, tsohon shugaban hukumar zabe da Farfesa Jibrin Ibrahim na Cibiyar Bunkasda Dimokiradiya dake Abuja da Auwal Musa Rafsanjani na Kungiyar CISLAC da kuma Dr Y. Z. Yau na Cibiyar CITAD dake Kano.

Sojojin Najeriya.
Sojojin Najeriya. premiumtimesng

Wasikar ta su tace kasashen Amurka da Faransa na ci gaba da tintibar hukumomin Njaeriya wajen samun amincewar su na girke dakaru a kasar saboda muhimmancin ta a yankin tekun Guinea, matakin da suka ce na iya haifar da barazanar tsaron cikin gida.

Fitattun 'yan arewacin kasar sun ce janye yarjejeniyar zaman sojojin kasashen 2 a Nijar saboda rashin taimakawa kasar ya jefa shakku a kan bukatar su ta zuwa Najeriya.

Wasikar tace babu wata nasarar da aka samu na girke wadannan sojoji a Nijar domin yaki da ta'addanci a Sahel ganin yadda matsalar sai kara ruruwa take yi.

Fitattun mutanen sun ce zaman sojojin Amurka a Nijar ya dace ya dinga taimakawa wajen dakile duk wani yunkurin kai hari, amma kuma sai aka samu akasin haka, matakin da ya nuna yadda matsalar ayyukan ta'addanci ke karuwa.

Wasikar ta gargadi shugabannin Najeriya a kan daukar duk wani mataki wanda ka iya zama barazana ga zaman lafiyar kasar baki daya ko kuma bangaren tsaron ta.

Ya zuwa yanzu dai gwamnatin Najeriya da kuma bangaren majalisun dokoki basu ce komai ba dangane da wannan wasikar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.