Isa ga babban shafi

Tubabbun mayakan Boko Haram sun kai farmaki ofishin ƴan sanda a Borno

A Najeriya, wasu tubabbun ƴan ƙungiyar Boko Haram sun kai farmaki wani ofishin ƴann sanda a Maiduguri, babban birni jihar Bornno da ke arewa maso gabashin ƙasar, a wani yunƙuri na ceto wasu abokansu da aka kama da laifin ta’ammali da muggan ƙwayoyi.

Un drapeau de Boko Haram (Image d'illustration).
Un drapeau de Boko Haram (Image d'illustration). © AFP/STEPHANE YAS
Talla

Sai dai jami’in hulɗa da jama’a  na rundunar ƴan sandan ta jihar Borno, Kenneth Doso,  wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin  ya ce jami’an ƴan sandan sun daƙile maharan.

Doso ya ce a ranar 30 ga watan Afrilu ne jami’an ƴsann sanda suka kai wani samame kasuwar Fara, biyo bayan bayanan sirri da suka samu na cewa wasu masu harkar muggan ƙwayoyi da tubabbbun ƴan Boko Haramm su na aikat ba daidai ba wajen, inda suka yi ram da wasu mutane 8 cikin su har, da mace guda, wadanda aka samu da gram 476 na  muggan ƙwayoyi.

Ya ce sa’o’i bayan kamen ne wasu tubabbun ‘yan Boko Haram, sanye da khakin soja suka yi ƙoƙarin kutsa kai cikin ofishin ‘’yan sanda da ke kan titin Ibrahim Taiwo, amma aka daƙile su ba tare da bata lokakci ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.