Isa ga babban shafi

Rundunar ‘yan sanda Najeriya ta kama wanda ya kitsa harin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kama wanda ake zargi hannu a harin da aka kai wa wani jirgin kasa da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna, mai suna Ibrahim Abdullahi wanda aka fi sani da Mande.

Jirgin da 'yan bindiga suka farwa a kan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Abujan Najeriya.
Jirgin da 'yan bindiga suka farwa a kan hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Abujan Najeriya. © dailytrust
Talla

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, Olumuyiwa Adejobi, wanda ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a Kaduna, ya ce an kama wanda ake zargin ne a gadar sama ta hanyar Abuja zuwa Kaduna daidai mahadar Rido.

A cewarsa, Mande ya amsa cewa shi ne shugaban kungiyar masu garkuwa da mutane da ke addabar babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.

A watan Maris din shekarar 2022 ‘yan bindiga suka farwa jirgin, yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Kaduna dagaa Abuja, inda suka yi garkuwa da mutane da dama, yayin da wasu kuma suka rasa rayukansu sakamakon harbin kan mai ‘uwa dawabi.

Adejobi Yya ce, wanda ake zargin ya taka rawa wajen yin garkuwa da mutane daban-daban da suka hada da garkuwa da mutane a Jami’ar Green Field baya ga kitsa kusan dukkanin sace-sacen da ake yi a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Rundunar ‘yan sandan ta kuma bayyana cewa jami’anta sun kama wani fitaccen shugaban kungiyar masu garkuwa da mutane wanda ya kitsa harin da aka kai a cocin Katolika na Saint Raphael a watan Satumban 2023 da ke garin Fadan Kamatan inda aka kona wani malamin addini da cocin kurmus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.