Tinubu zai koma gida Najeriya, bayan shafe mako guda ba'a ji duriyar sa ba
Bayan shafe mako guda ba tare da jin duriyar sa ba, shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu zai koma gida, kamar yadda mai taimaka masa na musamman kan yada labarai da dubaru Bayo Onanuga ya tabbatar.
Wallafawa ranar:
Rashin sanin takaimaiman hali ko kuma inda shugaban yake na tsahon mako guda ya fara haddasa cecekuce musamman game da yanayin lafiyar sa, yayin da aka fara nuna yatsa ga masu Magana da yawunsa tare da jifan su da tambayoyi kan inda shugaban yake.
Ganin karshe da aka yiwa Tinubu cikin bainar jama’a shine wajen taron tattalin arziki na birnin Riyadh din Saudi Arabiya, taron da ya halarta daga kasar Netherlands.
Ta cikin wani sako da ya wallafa a shafin sa na X Onanuga yace shugaban zai isa Najeriyar ne yau Laraba.
Jawabin na Onanuga dai bai yi karin bayani kan daga inda shugaban zai dawo ba, sai dai yace zai iso ne daga wata kasa ta Turai
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu