Isa ga babban shafi

Atiku ya bayyana damuwa a kan ficewar Tinubu da Shettima daga Najeriya

Najeriya – Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya bayyana damuwa a kan yadda shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakin sa Kashim Shettima suka fice daga kasar ba tare da barin wani jagora ba.

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya kenan Atiku Abubakar
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya kenan Atiku Abubakar © premium times
Talla

A wani tsokaci da ya wallafa a shafinsa na fezbuk, Atiku yace yana ta samun labaran dake nuna cewar shugaban da mataimakin sa sun fice daga Najeriya.

Atiku yace abin damuwa ne yadda wadannan shugabanni biyu zasu fice lokaci guda a kasar da ke fuskantar kalubale da dama.

Tsohon mataimakin shugaban yace abinda ke damun sa yanzu shine, wanene yake jan akalar kasar a wannan lokaci? Inda ya kara da cewar ko itace ke jagorancin kanta da kanta?

'Yan Najeriya na ci gaba da tsokaci a kan bacewar shugaba Bola Ahmed Tinubu kwanaki 7 da suka gabata, bayan halartar taron zuba jari a kasar Saudi Arabia.

Ya zuwa wannan lokaci babu wata sanarwa daga fadar shugaban a kan inda shugaban ya shiga, yayin da a yau kuma aka wayi gari da sanarwar cewar mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima zai tafi Amurka domin halartar wani taro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.