Isa ga babban shafi

Paris Saint Germain ta lashe gasar Ligue 1 ta Faransa kafin karkarewa

Kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint Germain ta lashe gasar Ligue 1 ta Faransa a bana, tun kafin a kai ga karkare gasar da tazarar maki 13, tsakaninta da ta biyu a saman Teburin.

'Yan wasan PSG na murnar lashe gasar League 1
'Yan wasan PSG na murnar lashe gasar League 1 REUTERS - Juan Medina
Talla

Nasarar ta PSG na zuwa ne bayan ta biyu a teburin gasar Monaco ta yi rashin nasara da ci 3 da 2 a gidan Lyon ranar Lahadi.

Yanzu haka dai saura wasanni uku kafin karkare gasar ta kakar nan, kuma nasarar da ta yi na nufin ta lashe kambun gasar har sau 12 kenan a tarihi.

Paris Saint-Germain players celebrate after winning League 1
Paris Saint-Germain players celebrate after winning League 1 REUTERS - Juan Medina

Wasu dai na ganin tun a ranar Asabar din da ta gabata ya kamata PSG din ta lashe kofin, amma sai ta tashi 3 da 3 a gida a wasan da suka fafata na mako na 31 da Le Havre.

Jumulla wannan shi ne kofin Ligue 1 da Paris Saint Germain ta dauka karo na 10 cikin kakar wasanni 11 da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.