Isa ga babban shafi

City ka iya sake daukar Firimiya bayan lallasa Nottingham Forest-Guardiola

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Pep Guardiola ya ce har yanzu akwai haske ga kungiyar a yunkurinta na lashe gasar Firimiyar Ingila karo na hudu a jere.

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Pep Guardiola
Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Pep Guardiola REUTERS - Violeta Santos Moura
Talla

Guardiola dai na wannan kalamaai ne jim kadan bayan kammala wasan da kungiyarsa ta buga da Nottingham Forest a ranar Lahadi.

Manchester City dai ta yi nasara kan Nottingham Forest da ci 2 da nema a wasan da suka fafata na mako nan.

Tuni dai masu sharhi ke kallon kalaman na Guardiola, a matsayin abinda zai iya kasancewa la’akhari da cewa kungiyarsa wasa na 34 ta buga, yayin da ta daya a saman teburin gasar Arsenal ita kuma ta buga wasanni 35.

Yanzu haka Manchester City wasanni hudu ne suka rage mata, yayin da ita kuma Arsenal wasanni uku ne suka rage mata a gasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.