Isa ga babban shafi

Juventus ta kai wasan karshe na gasar Coppa Italia bayan doke Lazio

Kwallon Milik ta bai wa Juventus damar samun tikiti a wasan karshe na cin kofin Coppa Italia bayan nasara kan Lazio da kwallaye 3 da 2 a jumulla, yayin haduwarsu ta daren jiya Laraba.

'Yan wasan Juventus.
'Yan wasan Juventus. © Marco BERTORELLO / AFP
Talla

Kwallon mai cike da kayatarwa, Arkadiusz Milik ya zura ta ne dakiku kalilan bayan sanya shi a fili ana minti na 83 da fara wasa wato gab da tashi ma kenan, kuma shi ne ya sauya akalar wasan tare da baiwa Juventus din nasara.

Bayan shan Kayenta da kwallaye 2 da nema a Turin, a farkon wasan Lazio ta farke dukkanin kwallayen biyu ta yadda ta sauya sakamakon zuwa kwallao 2 da nema a jumulla kuma 2 da 2, amma kuma shigowar Milik dan Poland ya sauya wasan.

Yanzu haka dai Juventus za ta yi dakon haduwa da ko dai Fiorentina ne ko Atalanta a wasan na karshe.  

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.