Isa ga babban shafi

Arsenal ta doke Chelsea da kwallaye 5 da nema a firimiyar Ingila

Arsenal ta doke Chelsea a karawarsu ta daren jiya karkashin gasar Firimiyar Ingila bayan ratata mata kwallaye 5 da nema, wanda ya baiwa tawagar ta Mikel Arteta damar kara yawan tazarar da take da shi a jagorancin teburin Firimiya da maki 3.

'Yan wasan Arsenal.
'Yan wasan Arsenal. REUTERS - Hannah McKay
Talla

Bayan nasarar ta jiya za a iya cewa Gunners ta farfado daga mummunan koma bayan da ta gani a makon jiya, ta yadda Aston Villa ta doke ta a gida karkashin gasar ta Firimiya a bangare guda Bayern Munich ta yi waje da ita daga gasar cin kofin zakarun Turai.

Farfadowar Arsenal ya sanyawa magoya baya kwarin gwiwar iya lashe kofin na Firimiya, duk da cewa tawagar na jagoranci ne da maki 77 biye da Liverpool mai maki 74 amma da wasa guda a hannu, ita kuma Manchester City da maki 73 da wasa biyu a hannu.

Har zuwa yanzu dai bata sauya zani ba game da tseren lashe kofin na Firimiya, lura da cewa cikin dukkanin kungiyoyin kowacce cikin kungiyoyin 3 ka iya lashe kofin, duk da cewa anfi bayar da karfi a Manchester City wadda dama ita ke rike kambun gasar, dai dai lokacin da ya rage wasanni 5 zuwa 6 a kammala kakar bana.

Yayin wasan na jiya Trossard ya fara zura kwallo a minti na 4 da taimakon Declan Rice yayinda Kai Harvertz da White kowannensu ya zura kwallaye bibbiyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.