Isa ga babban shafi

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester city ta yiwa Brighton wankan jego

A gasar Firimiyar Ingila inda ta kungiyar kwallon kafa ta Manchester ta yi wa abokiyar karawarta ta Brighton cin kacar tsohuwar keke, yayin da ta yi mata ci 4 da nema.

shahararren dan wasan Manchester city Haaland
shahararren dan wasan Manchester city Haaland © AFP - DARREN STAPLES
Talla

Firimiyar Ingila inda kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta samu nasara a wasan da ta kara da Brighton kuma ta yi mata cin kacar tsohuwar keke inda da ci 4 da nema har gida, wannan nasarar da Manchester ta samu ya kara wa kungiyar karsashi kan kokarin da ta ke yi na neman lashe gasar Firimiyar Ingila karo na 2 a jere, duk da cewa ta na a mataki na 2 a kan teburi da maki 76 inda Arsenal ta ke a mataki na farko da maki 77, sai dai har yanzu akwai kwantan wasa 1 daya da Manchester city ya rage ba ta buga ba shi ne wanda za ta kara da Notthingham Forest a ranar 28 ga watan Afirilu 2024, Arsenal da ta ke a mataki na 1 ta buga wasanni 34 daga cikin 38, har yanzu dai akwai aiki a gaban kungiyoyin 2, inda Arsenal a wasannin ta na gaba zata kara da Tottenham wanda yana cikin wasa mai zafi da kungiyar za ta yi, itama Manchester City za ta kara da Wolves a cikin wasannin da suka rage mata kuma wannan wasan ana hasashen zaiyi wahala ta samu nasara duba da yadda a tarihin kungiyoyin 2 wasanin da suka buga 22 Manchester city ta samu nasara 13 Wolves samu nasara 5 sun yi kunnen doki 4 kuma a jimilla Manchester city ta zura kwallaye 48 Wolves na 23 a nan za a iya cewa ba a san ma ci tuwo ba sai miya ta kare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.