Isa ga babban shafi

UEFA ta kara yawan 'yan wasan Tawagar kasashen Turai a gasar EURO

Hukumar kwallon kafa ta Nahiyar Turai UEFA, ta Amince da karin yawan 'yan wasan cikin Tawagar kasashe da zasu wakilci kasar su a gasar Kofin Nahiyar Turai na EURO 2024.

Tambarin gasar Europa
Tambarin gasar Europa REUTERS - DENIS BALIBOUSE
Talla

Hakan ya biyo bayan matakin da Jagororin hukumar su ka dauka a baya-bayan nan, Inda aka kara yawan 'yan wasan daga 23 zuwa 26, a kowacce tawagar kasa.

A baya dai hukumar ta UEFA, tare da hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA, na amfani da yawan 'yan wasan tawagar 22.

Sai dai daga bisani sun kara 'yan wasa dai-dai, inda ita kuma a yanzu sabon matakin da hukumar ta UEFA ta dauka ya amince da karin mutum uku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.