Isa ga babban shafi

Abba Gida-Gida ne ke mini bita da ƙullin siyasa - Ganduje

Shugaban jam’iyya mai mulkin Najeriya, wato Dakta Abdullahi Ganduje, ya ce jam’iyyar NNPP da ke mulkin jihar Kano ce, ke shirya masa bita da kullin siyasa, ciki kuwa har da zanga-zangar nuna adawa da kasancewarsa kan kujerar shugabancin APCn a Abuja.

Sai dai gwamnatin jihar ta Kano ta musanta cewa tana da hannu a rikicin da ya kunno masa.
Sai dai gwamnatin jihar ta Kano ta musanta cewa tana da hannu a rikicin da ya kunno masa. © dailytrust
Talla

Sai dai gwamnatin jihar ta Kano ta musanta cewa tana da hannu a rikicin da ya kunno masa.

An yi zanga-zangar neman a tsige Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar APC, inda kungiyoyi da jiga-jigan jam’iyyar daga yankin Arewa ta tsakiya ke kan gaba wajen adawa da salon mulkinsa.

A wata sanarwa da mai taimakawa Ganduje na musamman kan harkokin mu’amala da kungiyoyin fararen hula, Kwamared Okpokwu Ogenyi ya fitar, ta yi zargin cewa gwamnatin jihar Kano da daukar nauyin masu zanga-zangar, wadanda ta ce mafi yawancinsu ‘yan Kwankwasiyya ne, da suka fito daga daga shiyyar Arewa ta tsakiya da ke neman Ganduje yayi murabus.

Sanarwar ta kara da cewa, “Muna da sahihan bayanai cewa Gwamna Yusuf na aiki tare da wasu daga shiyyar Arewa ta tsakiya ta hanyar sakar musu makudan kudade domin kalubalantar tsohon gwamnan Kano Ganduje.

Yayin da yake kira ga jami’an tsaro da su sanya ido domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce masu zanga-zangar da aka dauki hayar su sun shiga sakatariyar jam’iyyar sanye da riga Kwankwasiyya.

A baya, mai magana da yawun gwamnan jihar Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya ce jam’iyyar NNPP, da gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, basu da wata alaka da rikicin da ke faruwa a tsakanin kowacce irin jam’iyya ce ta siyasa, abin da suka sanya a gaba shine, abubuwan da za su kawo wa jihar Kano ci gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.