Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

FIFA na iya dakatar da Najeriya

Hukumar Kwallon kafa ta duniya FIFA na iya dakatar da Najeriya saboda katsalandan da gwamnati ke yi ga sha’anin kwallon kafa musamman bayan wata Kotu ta dakatar da Majalisar Zartarwar hukumar NFF da ke kula da kwallon kafa a kasar.

Joseph Blatter, Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA
Joseph Blatter, Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA Foto: Reuters
Talla

Wani alkali a garin Jos a Jahar Flato mai suna PL Lot ya dakatar da shugaban Hukumar kwallon kafar Najeriya Aminu Maigari da daukacin 'yan majalisar zartarwa daga tafiyar da harkar kwallon kafa a kasar har sai ya kammala sauraron wata kara da aka gabatar masa.

Tuni kuma Ministan wasannin Najeriya Tammy Danagogo ya nada Lawrence Katiken, jami'i a hukumar a matsayin Kantoma na NFF.

Wannan na zuwa ne bayan Faransa ta yi waje da Najeriya a gasar cin kofin duniya a Brazil.

Hukumar FIFA ta taba yi Najeriya gargadin bayan wani mataki da gwamnatin Kasar ta so ta dauka na ficewa daga harakokin wasannin kwallon kafa na tsawon shekaru biyu tare da tube shugabannin hukumar NFF bayan Najeriya ta sha kashi a gasar cin kofin duniya da aka gudanar a kasar Afrika ta kudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.