Isa ga babban shafi
FIFA

FIFA ta dakatar da Najeriya

Hukumar FIFA ta dakatar da hukumar kwallon Najeriya saboda katsalandan da gwamnatin kasar ke yi wa sha’anin kwallon kafa. Wannan kuma na zuwa ne bayan wata kotu a Najeriya ta dakatar shugabannin hukumar NFF, inda nan take kuma gwamnati ta nada shugabannin rikon kwarya.

Dan wasan Najeriya Peter Odemwingie yana murna tare da abokan wasan shi bayan ya zira kwallo a ragar Bosnia a gasar cin kofin duniya a Brazil.
Dan wasan Najeriya Peter Odemwingie yana murna tare da abokan wasan shi bayan ya zira kwallo a ragar Bosnia a gasar cin kofin duniya a Brazil. REUTERS/Eric Gaillard
Talla

Wannan al’amari duka duka na zuwa ne bayan Faransa ta kori Najeriya a gasar cin kofin duniya a Brazil.

Idan dai har FIFA ba ta dage haramcin ba, matakin zai haramta wa Najeriya buga gasar cin kofin duniya ta mata ‘Yan kasa da shekaru 20 da za’a gudanar a kasar Canada a watan gobe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.