Jose Peseiro ya kawo karshen horas da Super Eagles ta Najeriya
Jose Peseiro ya bayyana kawo karshen aikinsa na horas da tawagar Najeriya Super Eagles.
Wallafawa ranar:
Dan kasar Partugal din, ya bayyana hakan ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, bayan watanni 22 yana jagorancin kungiyar.
A cewar Peseiro, ya kammala kwantiraginsa da hukumar kwallon kafa ta Najeriya a ranar Alhamis.
Kocin mai shekaru 63, wanda ya karbi ragamar horas da 'yan wasan a watan Yunin 2022 bayan Super Eagles ta kasa samun gurbin shiga gasar cin kofin duniya ta FIFA, ya jagoranci Najeriya zuwa matakin karshe a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2023 da ta gudana a kasar Ivory Coast, inda Najeriya ta zo na biyu a wasan yayin da Cote D’Ivoire da ta karbi bakunci ta lashe wannan gasa.
A halin da ake ciki kuma, ana danganta Peseiro da komawa horar da ‘yan wasan kasar Aljeriya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu