Isa ga babban shafi

Ingila ta rasa wakilci a manyan gasar zakarun Turai da Europa

Ingila ta rasa wakilci a manyan gasar zakarun Turai bayan ficewar kungiyoyin Arsenal da Manchester City da Liverpool da kuma West Ham daga gasar zakarun Turai da Europa a ranakun Laraba da Alhamis na makon nan.

Rashin tawaga daga Ingila a cikin manyan gasar Turai na rage karsashin wasanni.
Rashin tawaga daga Ingila a cikin manyan gasar Turai na rage karsashin wasanni. AFP/File
Talla

A ranar Larabar da ta gabata ne dai Bayern Munich ta fitar da Arsenal yayinda Real Madrid ta fitar da Manchester City dukkaninsu daga gasar zakarun Turai, gabanin ficewar Liverpool da West Ham a daren jiya, wanda ke nuna babu sauran wakilcin Ingila a manyan gasar 2 na Turai.

Bayern Lverkusen ce dai ta yi waje da West Ham daga gasar ta Europa duk da yadda suka yi canjaras a haduwar ta daren jiya da kwallo 1 da 1, amma da ya ke West Ham ta sha kaye da kwallaye 2 da nema a haduwarsu ta farko a makon jiya, hakan ya sanya tashi wasa a jumlace 1 da 3.

Kungiyar Manchester City mai rike da kambun gasar zakarun Turai da kuma Liverpool wadda wannan karon farko da ta ke samun kanta a gasar Europa cikin shekaru 8 da suka gabata, su aka yiwa tsammanin su iya fitar da Ingilar kunya a manyan gasar na Turai amma sai labari ya sha bamban.

Gasar zakarun Turai ita ke matsayin gasa mafi daraja a nahiyar ta Turai tsakanin kungiyoyi yayinda gasar Europa ke biye mata baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.