Isa ga babban shafi

Gaza lashe kofin zakarun Turai asara ce ga Bayern Munich - Kane

Dan wasan gaba na Ingila da ke taka leda da Bayern Munich ta Jamus, Harry Kane ya ce ko shakka babu wannan kakar za ta zamowa kungiyar tasa asara matukar ta gaza lashe kofin zakarun Turai.

Dan wasan gaba na Bayern Munich kuma kyaftin din tawagar Ingila Harry Kane.
Dan wasan gaba na Bayern Munich kuma kyaftin din tawagar Ingila Harry Kane. AFP - DANIEL ROLAND
Talla

Kane wanda ke wannan batu dai dai lokacin da suke shirin karbar bakoncin Arsenal a yau karkashin gasar zakarun Turai bayan da suka tashi wasa a makon jiya canjaras da kwallaye 2 da 2, ya ce har zuwa karawar ta daren yau suna da cikakkiyar damar sauya sakamakon don samun zarrar kaiwa wasan karshe na gasar tare da kuma lashe kofin.

Bayern Munich dai za ta tattara karfinta ne ga gasar ta cin kofin zakarun Turai bayan rasa Bundesliga, kofin da Bayern Leverkusen ta lashe a karshen makon jiya, duk da cewa akwai sauran wasanni.

Nasarar ta Leverkusen dai ta kawo karshen fatan Munich na lashe kofin karo na 12, kuma a yanzu haka kungiyar ba ta da muhimmin kofin da ya rage mata face na gasar ta zakarun Turai.

Tsohon tauraron na Tottenham wanda har zuwa yanzu bai taba lashe kofin wata gasa ba, ya ce ya na fatan tawagar ta shi ta yi aiki tukuru don kai labari a haduwar ta yau.

Zuwa yanzu Kyaftin din na Ingila mai shekaru 30 ya zurawa Bayern Munich kwallaye 39 a wasannin wannan kaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.