Isa ga babban shafi

Kotun wasanni ta bukaci Juventus ta biya Ronaldo dala miliyan 10

Kotun wasanni ta bukaci kungiyar kwallon kafa ta Juventus ta biya Cristiano Ronaldo na Portugal fiye da dala miliyan 10 da ke matsayin wani bangare na albashinsa da bai kai ga karba ba gabanin rabuwarsa da kungiyar ta Italiya.

Tauraron Portugal Cristiano Ronaldo da ke taka leda da Al Nassr ta Saudiya.
Tauraron Portugal Cristiano Ronaldo da ke taka leda da Al Nassr ta Saudiya. © LUSA - JOSE COELHO
Talla

Rahotanni sun bayyana cewa tun farko Ronaldo mai shekaru 39 da kansa ne ya zaɓi kin karbar albashin nasa a lokacin annobar corona lura da matsalar tatta arzikin da kungiyar ta samu kanta a ciki.

Kotun wasanni ta ce dole ne Juventus ta biya tauraron na Portugal da yanzu haka ke taka leda da Al Nassr ta Saudiya jumullar kudin na yuro miliyan 9 da dubu 800 dai dai da dala miliyan 10 da rabi wanda ke matsayin rabin adadin da Cristino ya ke bin kungiyar.

 Ronaldo wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or har sau 5 ya taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Juventus ne tsakanin shekarun 2018 zuwa 2021 inda ya taimakawa kungiyar lashe kofunan Serie A guda biyu amma ba tare da nasarar lashe kofin zakarun Turai ba, wanda saboda haka ne kungiyar ta sayo shi daga Real Madrid.

Sai dai kungiyar ta Juventus ta ce tawagar kwararrunta za su duba bukatar kotun gabanin sanar da mataki na gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.