Isa ga babban shafi
AFCON

Super Eagles za ta hadu da Ivory Coast a wasan karshe na gasar AFCON

Kai tsaye Super Eagles ta Najeriya za ta hadu da mai masaukin baki Ivory Coast a wasan karshe na cin kofin Afrika bayan nasararorin da kasashen biyu suka samu a wasanninsu na daren jiya Laraba, wasan karshen da zai gudana a ranar Lahadi 11 ga watan nan na Fabarairu.

Rabon Super Eagles da kaiwa wannan mataki tun a shekarar 2013 lokacin da ta lashe kofin gasar.
Rabon Super Eagles da kaiwa wannan mataki tun a shekarar 2013 lokacin da ta lashe kofin gasar. © AFP
Talla

Najeriyar dai ta doke Afrika ta kudu ne da kwallaye 4 da 2 a bugun fenariti yayin wasan gab da karshe karkashin gasar ta AFCON a jiya, nasarar da ta kawo ta wannan mataki na wasan karshe wanda rabonta da kai wa tun a shekarar 2013 wanda kuma ta lashe kofin a wancan lokaci.

A bangare guda Ivory Coast ta yi nasarar kaiwa wasan karshen ne bayan doke jamhuriyyar Demokradiyyar Congo da kwallo 1 mai ban haushi.

Wannan nasara ta nuna yadda Super Eagles ta doke Bafana-Bafana sau 3 a jere yayin mabanbantan wasannin wannan gasa ta AFCON ciki har da dukan da ta yi mata a filin wasa na Lagos cikin shekarar 2000.

Gabanin lashe kofinta a 2013 ko a shekarar 2000 Super Eagles ta kai wasan karshe na AFCON lokacin da Najeriya ta yi hadin gwiwa da Ghana wajen daukar nauyin gasar bayan da Zimbabwe ta gaza dauka.

A jumulla dai wasan karshen da zai gudana ranar Lahadi tsakanin Najeriyar da Ivory Coast na nuna yadda Super Eagles za ta taka leda a wasan karshe na gasar karo na 8.

Najeriya dai ta hadu da Ivory Coast a matakin rukuni inda ta doke ta da kwallaye 2 da nema.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.