Isa ga babban shafi

Fitilar gasar Olympic ta bana ta iso birnin Paris

Dubun dubatan jama'a ne suka hallara a wannan Laraba a birnin Marseille da ke kudanacin Faransa domin tarbar fitilar  gasar Olympics a wani yunkuri na sake kafa wani tarihi a daidai lokacin da gasar ke karatowa wadda birnin Paris zai karbi bakwanci.

Jiragen sama sun yi wasa wasan tartsatsin launuka a yayin isowar jirgin ruwa dauke da wutar gasar Olympic.
Jiragen sama sun yi wasa wasan tartsatsin launuka a yayin isowar jirgin ruwa dauke da wutar gasar Olympic. REUTERS - Benoit Tessier
Talla

Wani katafaren jirgin ruwa mai tutoci uku ne ya yi dakon wannan wutar ta Olympic daga Girka zuwa tsohuwar tashar jiragen ruwa ta Marseille yayin da aka rera taken ƙasar Faransa.

Wani jirgin saman sojin sama ya yi ta shawagi a sararin samaniya domin alamta halartowar jirgin ruwan dauke da fitilat ta Olympic, yayin da wasu jiragen sama na daban suka zana awarwao guda biyar da ke matsayin tambarin gasar Olympic kafin su kuma fitar da launukan ja da shuɗi da fari, wato launin tutar Faransa.

Dubban mutane ne suka yi dandazo a kan tantagaryar kasa kusa da gabar ruwa domin murnar tarbar fitilar, sannan ga kuma karin wani adadi mai yawa na jama'a da suka kalli bikin tarbar ta tagogi da saman benaye.

Mawakin gambara Julien Mari ne ya kunna wutar gasar ta Olympic a Marseille.
Mawakin gambara Julien Mari ne ya kunna wutar gasar ta Olympic a Marseille. © AFP - CHRISTOPHE SIMON

Mawakin gambara dan asalin Marseille, Jul shi ne ya kunna fitilar gasar ta Olympic bayan Florent Manaudou shi ma dan asalin Faransa da ya lashe tseren ninkayar mita 50 na maza a Olympic ta 2012, ya dauko mariƙin fitilar zuwa tantagaryar kasa daga cikin jirgin ruwan.

A yayin isowarsa Marseille, shugaban Faransa Emmanuel Macron ya gana da ƴan wasan tsalle-tsalle na Olympic da suka yi wa fitilar rakiya a cikin jirgin ruwan wanda aka ƙera a ƙarni na 19.

Shugaba Macron a yayin jawabinsa ya bayyana cewa,

Tun da wannan wutar ta iso, Faransa ta shiga cikin wasannin.

Masu shirya gasar na fatan ƴan kallo na sahun farko za su taimaka wajen ɗabbaƙa zumudin gasar bayan matsalar da aka samu dangane da ƙudin tiket da kuma batun samar da tsaro a yayin gudanar da gasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.