Isa ga babban shafi

Julen Lopetegui ya amince da karbar aikin horar da West Ham United

Julen Lopetegui ne ya amince da karbar ragamar horar da kungiyar kwallon kafa ta West Ham United mai doka firimiyar Ingila.

Julen Lopetegui, duk da rashin gagarumar nasara yayin horar da Real Madrid, amma ya yi nasarar lashe kofin Firimiya a Sevilla.
Julen Lopetegui, duk da rashin gagarumar nasara yayin horar da Real Madrid, amma ya yi nasarar lashe kofin Firimiya a Sevilla. POOL/AFP/Archives
Talla

Duk da cewa Lopetegui bai sanya hannu kan kwantiragi da Hammers ba, amma ya bayar da tabbacin karbar aikin a karshen wannan kaka wanda zai baiwa manajan mai shekaru 57 damar komawa firimiya bayan ajje aikin horar da Wolves a watan Agustan bara.

Matakin wanda ita kanta West Ham ta sanar na zuwa ne a wani yanayi da manajan kungiyar David Moyes ke tsaka mai wuya bayan rashin nasara a wannin firimiya 8 cikin 9 da ya doka a baya-bayan nan ciki har da ragargazar da Cheslea ta yi mata a karshen mako da kwallaye 5 da nema.

Haka zalika tawagar ta Moyes ta yi wulakantacciyar ficewa daga gasar Europa duk dai a makon na jiya.

Moyes wanda dama ya ke da tantama game da makomarshi a kungiyar ya ce sai bayan wasan karshe tsakaninsu da Manchester City na ranar 19 ga watan Mayu ne zai tabbatar da yiwuwar rabuwa da kungiyar duk da cewa dama a lokacin ne kwantiraginsa zai kawo karshe.

A bangare guda Lopetegui wanda ya taba horar da Real Madrid ya lashe kofin Europa da Sevilla a kakar wasa ta 2020.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.