Isa ga babban shafi

Manchester United ta gaza kai banten ta a hannun Crystal Palace

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta kasa samun gurbin komawa cikin masu fatan buga gasar zakarun Turai a badi, a wasan da suka doka da Crystal Palace na gasar Firimiyar kasar Ingila a daren jiya Litinin.

Mai horas da kungiyar Kwallon kafa ta Manchester united, yayin da yke jimamin zurawa kungiyarsa Kwallaye
Mai horas da kungiyar Kwallon kafa ta Manchester united, yayin da yke jimamin zurawa kungiyarsa Kwallaye © RFI
Talla

Wasan wanda shi ne na mako na 36 Crystal Palace ta yi wa Man United dakan sakwarar Legas 4-0, wanda hakan shi ya kawo wa United din tazgaro ga fatanta na buga gasar Zakarun Turai ta badi.

Har yanzu dai Arsenal ce ke matsayin ta 1 a saman Teburin gasar Firimiyar ta Ingila, sai Manchester City da ke matsayin ta 2, kuma maki daya ne kadai tsakaninsu.

Masu sharhi kan wasanni na ganin dama City din ta yi shuhura wajen shan kai, sai sauran kungiyoyi sun gama dako sai ta karba a karshe.

Kazalika wasu na ganin Manchester City din ka iya kara lashe kofin a bana, la'akhari da a yanzu haka tana da kwantan wasa daya, ko da yake wasu na ganin itama Arsenal din a bana ta fito da karfinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.