Isa ga babban shafi

Najeriya ta tsallaka wasan karshe a gasar AFCON

A karon farko cikin shekaru 10, tawagar kwallon kafa ta Super Eagles ta Najeriya ta tsallaka wasan karshe na gasar cin kofin Afrika da ke gudana a Ivory Cost bayan ta casa Afrika ta Kudu a bugun fanariti.

'Yan wasan Najeriya a yayin murnar samun nasara
'Yan wasan Najeriya a yayin murnar samun nasara © AFP / ISSOUF SANOGO
Talla

Kasashen biyu sun shafe tsawon sa'o'i 120 suna gumurzu 1-1 kafin daga bisani su buga fanariti, inda Najeriyar ta samu nasara da kwallaye 4-2.

Mai tsaren ragar Najeriya, Stanley Nwabali ya taka gagarumar rawa wajen tare kwallaye biyu da 'yan wasan Afrika ta Kudu suka buga masa a bugun na fanariti, abin da ya sa ya zama gwarzon wasan.

Najeriya za ta buga wasan karshe tsakaninta da Ivory Coast ko kuma Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo, kasashen da a yanzu haka ke kan fafatawa da juna.

Masharhanta kan kwallon kafa sun sanya Najeriya cikin kasashen da ke kan gaba wajen yiwuwar lashe babbar gasar ta kwallon kafa a Afrika.

Rabon da Najeriya ta lashe gasar ta AFCOn tun shekarar 2013, lokacin da ta doke Burkina Faso da ci 1-0 a Afrika ta Kudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.