Isa ga babban shafi

Kungiyar PSG ta kama hanyar lashe kofin gasar ligue 1 karo na 12

Tauraruwar Goncalo Ramos ta haska a nasarar da PSG ta yi kan kungiyar kwallon kafa ta Lyon bayan da ya ratata kwallaye har 2 a raga yayin wasan da suka yi nasara da kwallaye 4 da 1 a gida, wanda ya basu damar kara tazarar maki 11 a saman teburin gasar ta Ligue 1.

'Yan wasan PSG bayan nasararsu ta fitar da Barcelona daga gasar cin kofin zakarun Turai.
'Yan wasan PSG bayan nasararsu ta fitar da Barcelona daga gasar cin kofin zakarun Turai. REUTERS - Juan Medina
Talla

Wasan wanda ya gudana ba tare da tauraron kungiyar ta birnin Paris ba wato Kylian Mbappe bayan da mai horarwa Luis Enrique ya ke ci gaba da wasanni ba tare da shi ba, saboda abin da ya ce dole kungiyar ta koyi wasa ba tare da tauraron ba, lura da yadda ya ke shirin raba gari da ita a karshen kaka.

Tun farko Nemanja Matic na Lyon ne ya yi kuskuren zura kwallo a ragarsu wanda ya bai wa PSG jagoranci da kwallo 1 da nema gabanin kwallon Lucas Beraldo sai kuma shi Ramos da ya zura kwallaye har 2 a haduwar ta jiya.

Da kwallayen na Goncalo Ramos dan Portugal kai tsaye PSG ta kama hanyar sake lashe kofin na Ligue 1 bayan da ta ke jagoranci da maki 11 biye da Monaco dai dai lokacin da ya rage wasanni 5 a karkare wasannin kaka.

Ramos na sahun 'yan wasan da ake ganin ya iya maye gurbin Mbappe a kaka mai zuwa wajen ci gaba da cirewa kungiyar kitse a wuta lura da yadda ya ke haskawa da zarar PSG ta doka wasa ba tare da tauraron na Faransa ba.

Duk da cewa har yanzu babu tattaunawa a hukumance da ta amince da tafiyar Mbappe Real Madrid, amma dan wasan da kansa ya nanata cewa tabbas zai raba gari da PSG a karshen wannan kaka.

Kakar wasa biyu a jere Mbappe ya shafe ya na son rabuwa da kungiyar wadda ta sayo shi daga Monacco amma ya na gaza tafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.