CAF ta amince da sunayen 'yan wasa da Najeriya ta gabatar su je gasar AFCON
Hukumar kula da kwallon kafar Afrika CAF ta amince da sunayen tawagar ‘yan wasan wucin gadi na Super Eagles ta Najeriya da za su taka leda a gasar cin kofin Afrika ta 2023 kamar yadda kocin kungiyar, Jose Peseiro ya mika mata.
Wallafawa ranar:
CAF ta tabbatar da jerin sunayen kamar yadda aka bayyana a shafin yanar gizon ta jiya Laraba.
Ana sa ran Peseiro ya gabatar da cikakkiyar tawagarsa ta karshe ga hukumar ta CAF kafin wa'adin da aka diba ya kare a ranar 3 ga watan Janairu.
A cikin jerin sunayen akwai ‘yan wasa uku da ke taka leda a cikin gida – Ojo Oluwasegun (Enyimba FC), Christian Nwoke (Sporting Lagos FC) da Obasogie Amas (Bendel Insurance).
Bayan hukunci da kwamitin shirya gasar CAF na AFCON ya yanke, za a ba wa dukkanin kungiyoyi 24 izinin shigar da jerin ‘yan wasa 27 na karshe, wanda ya zarce 23 da aka buga gasar a baya.
Za’a soma gasar ce daga ranar 13 ga watan Janairu zuwa 11 ga watan Fabrairu, 2024, a garuruwan Abidjan, Bouake, Korhogo, San Pedro da Yamoussoukro na kasar Ivory Coast.
Jerin sunayen 'yan wasan wucin gadi na Najeriya:
Francis Uzoho
Temitayo Aina
Jamilu Collins
Ndidi Wilfred
William Ekong
Ajayi Adesewo
Ahmed Musa
Ogochukwu Onyeka
Victor Osimhen
Ayodele-aribo Oluwaseyi
Samuel Chukwueze
Ademola Lookman
Zaidu Sanusi
Kelechi Iheanacho
Musa Saminu
Adebayo Adeleye
Calvin Ughelumba
Alexander Iwobi
Sadiq Umar
Awaziem Collins
Tyronne Ebuehi
Kenneth Omeruo
Ojo Oluwasegun
Akpoguma Ufuoma
Victor Boniface
Onyemaechi Bruno
Samuel Bright
Bonaventure Dennis
Ebere Onuachu
Terem Moffi
Sunan mahaifi Cyriel
Tela Temitayo
Nwadike Onyedika
Oluwafisayo Dele-Bashiru
Torunarigha Jordan
Alhassan Abdullahi
Kelechi Nwakali'
Christin Nwoke
Stanley Nwabali
Obasogie Amas
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu