Isa ga babban shafi

Xavi zai ci gaba da jagorantar Barcelona har zuwa 2025

Kocin Barcelona Xavi ya yi amaia ya lashe, yayin da ya ce zai ci gaba da zama a kungiyar har zuwa karshen kwantiraginsa a watan Yunin 2025 bayan ya bayyana ra’ayinsa cewa wannan ce kakarsa ta karshe.

Mai horas da kungiyar Kwallon kafa ta Barcelona Xavi kenan.
Mai horas da kungiyar Kwallon kafa ta Barcelona Xavi kenan. REUTERS - Sarah Meyssonnier
Talla

Kocin mai shekaru 44 ya sanar a watan Janairu cewa zai ajiye mukamin horas da ‘yan wasan kungiyar a bana.

Sai dai ana ganin bisa kaimin shugaban kungiyar, Joan Laporta na son ya ci gaba da kasancewarsa, tsohon dan wasan tsakiyar na Barcelona da Spain ya yanke shawarar ci gaba da zama har zuwa 2025.

Xavi ya karbi ragamar horar da Barcelona a watan Nuwambar 2021 bayan ya bar kungiyar Al Sadd ta kasar Qatar.

A halin da ake ciki yanzu tazarar maki 11 ne tsakaninta da Real Madrid wadda ke jagorantar teburin La Liga, inda ya kasance saura wasanni shida a kammala wannan kaka ta bana.

A makon da ya gabata ne Barcelona ta fice daga gasar zakarun Turai bayan ta sha kashi a hannun Paris St-Germain a wasan kusa da na karshe.

Karkashin jagorancin Xavi, Barcelona ta buga wasanni 10 ba tare da an doke ta a La ligar bana ba, kafin ta sha kashi a hannun Real Madrid da ci 3-2 a ranar Lahadin da ta gabata.

Ana ganin idan har Xavi ya gaza sauya salon yadda kungiyar ke tafiya daga nan zuwa karshen kakar wasa ta 2024-25, Barcelona za ta yi kokarin kawo daya daga cikin manyan masu horaswa, irin su Pep Guardiola, Luis Enrique ko kuma Mikel Arteta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.