Isa ga babban shafi

Najeriya na dab da sallamar kocin Super Eagles

Rahotanni daga Najeriya, hukumar kwallon kafar kasar ta fara laluben wanda zai maye gurbin mai horas da tawagar ‘yan wasan kasar Super eagles, wato Jose Peseiro, yayin da take duba yuwuwar sallamar sa.

Jose Peseiro lokacin da yake horas da kungiyar FC Porto.
Jose Peseiro lokacin da yake horas da kungiyar FC Porto. © Reuters
Talla

Kwamitin gudarwar hukumar, y ace bai gamsu da yadda kocin ke jagorantar Super eagles ba, inda ya yanke shawarar nemo mai haoraswa daga cikin gida.

Tun lokacin da Kocin dan kasar Portugal ya karbi jahgorancin kungiyar a shekarar 2022, wasanni shida kacal ya samu nasara a kai, inda yayi rashin nasara a wasanni 15.

Shugaban kwamitin, Shariff Ahlan yayin wata ganawa da manema labarai, y ace idan har yana da cikakken ikon sallamar wannan mai horaswa da tuni ya daga masa jan kati, domin kuwa yadda yake jagorantar kungiyar babu abin a yaba a ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.