Isa ga babban shafi
FIFA

FIFA zata tsaurara hukunci akan nuna wariya

Sepp Blatter da ke Shugabantar hukumar kula da sha’anin kwallon kafa a duniya FIFA ya yi kiran a dauki tsauraran matakai akan duk kungiya ko dan wasa da aka kama da laifin nuna wa wani wariyar launi fata a filin wasa.

Joseph Blatter, Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA
Joseph Blatter, Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA Foto: Reuters
Talla

Blatter ya fadi haka ne a babban zauren taron mambobin hukumar kwallon Afrika a birnin al Kahira na Masar

Bakaken fata dai na fuskantar matsalar wariya a Turai, lamarin da wasu masu sharhi ke ganin akwai sakaci daga mahukuntan kwallon kafa na rashin daukar matakai masu tsauri don yakar matsalar.

Amma Blatter ya ce yanzu hukuncin ba zai tsaya kawai daga cin tarar dan wasa ba ko kungiya ko haramta buga kwallo a filin wasa, yanzu za su dauki matakin dakatar da kungiya tare da datse makin da ta samu, da korar kungiya zuwa mataki na biyu na league idan har matsalar ta yi girma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.