Isa ga babban shafi
Kwallon Kafa

Amurka na son FIFA ta dauki mataki akan Rasha

Wasu ‘Yan Majalisar Dattijan Amurka sun bukaci hukumar FIFA ta haramta wa kasar Rasha damar daukar nauyin gasar cin kofin duniya a 2018 saboda rawar da ta taka a rikicin kasar Ukraine musamman ballewar yankin Crimea.

Joseph Blatter, Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA
Joseph Blatter, Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA DR
Talla

‘Yan Majalisar Amurka 13 ne daga bangaren Jam’iyyar Republican da Democrat suka rubutawa hukumar FIFA bukatar a dakatar da ba rasha damar karbar bakuncin gasar.

A cewarsu ba Rasha dama zai kara ba shugaban kasar Vladimir Putin girma a idon duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.