Isa ga babban shafi
FIFA

‘Yan takara uku za su kalubalanci Blatter a Zaben FIFA

Kwamitin shirya zaben hukumar FIFA ya amince da takarar Sepp Blatter da kuma wasu mutane uku da za su kalaubalanci shugaban na hukumar kwallon duniya. Kwamitin ya ce dukkanin ‘yan takarar sun cancanci tsayawa takarar zaben shugabancin hukumar da za a gudanar a ranar 29 ga watan Mayu.

Luis Figo na Portugal
Luis Figo na Portugal
Talla

Blatter wanda ya kashe shekaru kusan 17 yana shugaban FIFA, a bana ‘yan takara uku ne zasu kalubalance shi a zaben hukumar wadanda suka hada da shugaban hukumar kwallon Holland Michael van Praag, da mataimakinsa a yankin Asia Yariman Jordan Ali bin Al Hussein, da kuma tsohon zakaran kwallon duniya Luis Figo.

Dole dai sai Dan takara ya samu rinjayen kuri’u na mambobin FIFA 205 kafin ya lashe zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.